Daga Umar dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan ayyuka (ba sa yiwu...
Ingantacce ne
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a ci...
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya farar da (wani abu) daga al'...
Ingantacce ne
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nu...
Daga Umar ɗan khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayi...
Ingantacce ne
Muslim ne ya rawaito shi

Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da s...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "An gina musulunci abisa a...
Ingantacce ne
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar...
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair...
Ingantacce ne
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bay...

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a cikin dukkanin ayyuka na ibadu da mu'amaloli, wanda ya yi nufin wani abin amfani da aikinsa ba zai samu komai ba sai wannan abin amfanin, kuma babu sakamako gareshi, wanda yayi nufin neman kusanci da aikinsa zuwa ga Allah - madaukakin sarki zai samu sakamako da lada daga aikinsa ko da aikin ya kasance na al'ada ne, kamar ci da sha. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don bayanin tasirin niyya a ayyuka tare da daidaituwarsu a sura ta zahiri, sai ya bayyana cewa wanda ya yi nufin neman yardar Ubangigjinsa da hijirarsa, to, hijirarsa hijira ce ta shari'a abar karɓa za a yi masa sakayya a kanta don gaskiyar niyyarsa, wanda ya yi nufin wani abin amfani na duniya na dukiya, ko kasuwanci, ko mata da hijirarsa ba zai samu komai daga hijirarsa ba sai wancan abin amfanin da ya yi niyyarsu, kuma ba zai samu lada da sakamako ba.
Hadeeth details

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.
Hadeeth details

Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a surar wani mutum namiji ba a sanshi ba, daga siffofinsa cewa tufafinsa masu tsananin fari ne, gashin kansa kuma mai tsananin baƙi ne, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi na bayyanar gajiya, da ƙura, da rarrabewar gashi, da dattin tufafi, kuma wani ɗaya daga mahalartan bai sanshi ba, alhali su suna zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai neman sani, sai ya tambayeshi game da musulunci, sai ya ba shi amsa da waɗannan rukunan, waɗanda suka ƙunshi iƙirari da shaida biyu, da kiyayewa a kan salloli biyar, da ba da zakka ga waɗanda suka cancanta, da azimin watan Ramadan, da ba da farillar Hajji a kan mai iko. Sai mai tambayar ya ce: Ka yi gaskiya, sai sahabbai suka yi mamaki daga tambayarsa mai nuni a kan rashin saninsa a cikin abin da yake bayyana da kuma gasgatashi. Sannan ya tambayeshi game da imani, sai ya amsa masa da waɗannan rukunan guda shida masu ƙunshe da imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da siffofinsa, da kaɗaitashi da ayyukansa kamar halitta, da kaɗaitashi da ibada, kuma cewa mala'iku waɗanda Allah Ya haliccesu daga haske bayi ne ababen girmamawa ba sa saɓawa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma suna aiki da umarninsa, da yin imani da littattafan da aka saukar ga manzanni daga Allah - maɗaukakin sarki -, kamar Al-ƙur'ani da At-Taura da Injila da wasunsu, da kuma (imani) da manzanni masu isar da Addinin Allah, daga cikinsu akwai Nuhu, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da na ƙarshensu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -, da wasunsu daga Annabawa da manzanni, da imani da ranar lahira, abin da ke bayan mutuwa yana shiga cikinsu na kabari da rayuwar barzahu, kuma cewa mutum za a tasheshi bayan mutuwa kuma za a yi masa hisabi, kuma makomarsa za ta zama ko dai zuwa aljanna ko zuwa wuta, da imani da cewa Allah Ya ƙaddara abubuwa gwargwadon yadda iliminsa ya rigaya da shi, kuma hikimarsa ta hukuntashi da rubutunsa ga hakan, da mashi'arsa gareshi, da afkuwarsu gwargwadon yadda ya ƙaddarasu, ya kuma haliccesu don haka. Sannan ya tambayeshi game da kyautatawa, sai ya ba shi labari da cewa kyautatawa ita ce ya bautawa Allah kamar shi yana ganinsa, idan bai samu damar kaiwa zuwa wannan matsayin ba, to, ya bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - kamar Allah Yana ganinisa, na farko shi ne matsayin Mushahada, ita ce mafi ɗaukaka, na biyu shi ne matsayin Muraƙabah. Sannan ya tambayeshi yaushe ne al-ƙiyama? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa sanin al-ƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa, babu wani daga halitta da ya sanshi, wanda ake tambayar da mai tambayar. Sannan ya tambayeshi game da alamomin al-ƙiyama? Sai ya bayyana masa cewa daga alamominta akwai yawan kuyangi (sa-ɗaka) da 'ya'yansu, ko yawan saɓawar 'ya'ya ga iyayensu, mata za su dinga yi musu mu'amala irirn mu'amalar bayi, kuma cewa makiyaya dabbobi da talakawa za a shinfiɗa musu duniya a ƙarshen zamani, sai su dinga alfahari a ƙawata gine-gine da ɗaukakasu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labari da cewa mai tambayar shi ne Jibrilu ya zo don sanar da sahabbai wannan addinin miƙaƙƙe.
Hadeeth details

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.
Hadeeth details

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa Shi kadai kada su hada shi da wani abu. Kuma cewa hakkin bayi ga Allah shi ne ba zai azabtar da masu kadaitaShi da bauta ba, wadanda ba sa sanya masa abokin tarayya ba. Sannan cewa Mu'az, ya ce: Ya Manzon Allah, shin baa a yi wa mutane albishir da shi ba dan su yi farinciki, kuma su yi murna da wannan falalar ba ?? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana shi dan tsoron kada su dogara akanta.
Hadeeth details

Mu’azu Ɗan Jabal Allah Ya yadda da shi, ya kasance yana bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan abin hawa na dabbarsa, sai ya kira shi Ya Mu’azu, ya maimaita kiran na sa har sau uku, domin ƙarfafawa da Kuma muhimmancin abin zai faɗa masa. A duka kiran Mu’azu Allah Ya yarda da shi yana amsa masa da cewa; Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da da farincin hakan bayan farinciki, Wato na amsa maka Ya Ma’aikin Allah bayan amsawa, kuma na nemi farinciki da wannan amsawa. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba shi bayanin babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Ma’aikin Allah ne da gaske daga zuciyarsa ba ƙarya ba, idan har ya mutu a wannan hali, to, Allah Ya haramta masa wuta. Sai Mu’azu Allah Ya yarda da shi ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan ya baiwa mutane labari domin su yi farin ciki su yi wa juna bushara ta alheri? Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji tsoron kada su saki jiki da hakan, su ƙaranta ayyuka. Mu’azu bai ba da wannan bayanin ba sai dab da rasuwarsa, don tsoron kada ya faɗa cikin masu ɓoye ilimi.
Hadeeth details

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin wanda ya faɗa kuma ya shaida da bakinsa: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya kafircewa abin da ake bautawa da ba Allah ba, ya barranta da dukkanin addinai ban da Musulunci, to, haƙiƙka dukiyarsa da jininsa sun haramta a kan Musulmai, ba abin da muke da shi sai zahirin aikinsa, ba za a kwace dukiyarsa ba, ba za a zubar da jininsa ba, sai dai idan ya aikata wani laifi, ko ɓarna da za ta tabbatar da hakan a Hukunce Hukuncen Musulunci. Allah Shi ne Yake jiɓintar hisabinsa ranar Alƙiyama, idan ya yi da gaskiya a ba shi lada, idan kuma munafiki ne a yi masa azaba.
Hadeeth details

Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da dabi'u biyu: Wacce take wajabta shiga Aljanna, da wacce take wajabta shiga wuta? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa: Cewa dabi'ar da take wajabta Aljanna ita ce mutum ya mutu alhali yana bautawa Allah Shi kadai ba ya taranya wani abu da shi, Kuma cewa dabi'ar da take wajabta wuta ita ce mutum ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah, sai ya sanya kishiya ga Allah da tamka a cikin AllantakarSa ko a kasancewar shi ne Mahalicci ko sunayenSa da siffofinSa.
Hadeeth details

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bamu labarin cewa wanda ya karkatar da wani abu daga abinda yake wajaba ya zama na Allah ne zuwa waninSa, kamar rokon wanin Allah - Madaukakin sarki - ko neman agaji ga waninSa, ya kuma mutu akan hakan to cewa shi yana daga 'yan wuta. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya kara cewa wanda ya mutu alhali ba ya hada wani abu da Allah to makomarsa tana aljanna.
Hadeeth details

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki Mu'azu Dan Jabal zuwa garuruwan Yaman yana mai kira zuwa ga Allah kuma mai ilimantarwa, ya bayyana masa cewa shi zai fuskanci wasu mutane daga Nasara; dan ya zama akan yi musu tanadi, sannan ya fara da mafi muhimmaci sannan mafi muhimmanci a kiran nasu, Sai ya kirasu zuwa gyara akida a farko; da cewa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne; Domin cewa da ita ne za su shiga Musulunci, idan sunyi imani da hakan sai ya umarcesu da tsaida sallah' domin cewa ita ce mafi girman wajibai bayan Tauhidi. Idan sun tsaida ita sai ya umarci mawadatan su da bada zakkar dukiyoyin su zuwa talakawansu, sannan ya gargade shi daga karbar mafificiyar dukiya; domin cewa wajibi shi ne tsaka-tsakiya, Sannan yayi masa wasicci da nisantar zalinci' dan kada wanda aka zalinta yayi masa mummunar addu'a domin cewa addu'arsa abar karbace.
Hadeeth details

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafi azirtar mutane da cetansa a ranar alkiyama shi ne wanda ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa". Wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya zama kubutacce daga shirka da riya.
Hadeeth details

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewar imani rassa ne, kuma halaye ne masu yawa, sun kunshi ayyuka da ƙudurce-ƙudurcen zuciya da maganganu. Kuma mafi girman ɗabi’un imani da falala shi ne faɗin: "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah". Tare da sanin ma’anarta, da kuma aiki da abin da take nunawa na cewa Allah Shi ne abin bauta guda ɗaya, wanda Ya cancanci a bauta masa Shi kaɗai ban da wani ba shi ba. Kuma mafi ƙarancin ayyukan imani shi ne kawar da duk abin da zai cutar da mutane a kan hanyoyi. Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin cewa kunya tana cikin ɗabi’u na imani, kuma ɗabi’a ce da take zaburarwa a kan yin abu mai kyau da kuma barin mummuna.
Hadeeth details