Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji* a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula.
[سورة البقرة
] • 197
To, idan kun ƙãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: "Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wanirabo a cikin Lãhira.
[سورة البقرة
] • 200
Waɗannan suna da rabo daga abin da suka sanã'anta; kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.
[سورة البقرة
] • 202
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
[سورة المائدة
] • 2
"Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci."
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".
Ingantacce ne
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi".
Ingantacce ne
Buhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ke kan abin hawa shi ke sallama ga mai tafiya, mai tafiya kuma yana sallama ga wanda ke zaune, kadan kuma (suna sallama) ga masu yawa".
Ingantacce ne
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo".
Ingantacce ne
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wani mutum yana yi wa ɗan uwansa wa'azi game da kunya, sai ya ce: "Kunya tana daga imani".